Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Hukumar INEC Ta Soke Rijistar Zabe Miliyan Uku

Hukumar za?e ta ?asa ta ce kashi 40 cikin 100 na sabbin wa?anda ta yi wa rajistar katin jefa ?uri’a ?alibai ne, tana mai cewa ta soke rajista kusan miliyan uku da suka sa?a wa ?ai’dojin hukumar.

Shugaban hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ?ara da cewa kashi 76 cikin 100 na masu za?e a ?asar matasa ne.

A cewarsa yayin wani taro da jam’iyyun siyasa a Abuja ranar Laraba, an samu ?arin masu katin jefa ?uri’a 9,518,188 a kan 84,004,084 da ake da su, kuma a yanzu rajistar farko-farko ta nuna cewa jimillar adadinsu ya kai 93,522,272.

“Bayan kammala aikin, mutum 12,298,944 ne suka yi rajistar. Amma tun tuni mun sha fa?a cewa hanyoyinmu na tsaftace rajistar masu inganci ne,” in ji shi.

“Bayan mun tantance bayanan ta hanyar amfani da tsarin Automated Biometric Identification System (ABIS), mun gano 2,780,756 (kashi 22.6 cikin 100) ba su cancanta ba kuma muka goge su. Cikinsu akwai wa?anda suka yi sau biyu, da yaran da ba su kai ba, da kuma ma na boge wa?anda ba su cika ?a’idojinmu ba.”

A watan Fabarairu na 2023 ne INEC za ta gudanar da babban za?e a Najeriya, inda ‘yan ?asa za su za?i sabon shugaban ?asa da gwamnonin jiha da ‘yan majalisar jiha da na tarayya.

Exit mobile version