Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da ?ir?irar karin rumfunan zabe dubu 56,872 a fadin kasar.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wani taro da ya yi da kwamishinonin zabe na jihohi a ranar Laraba.
Hakan na nufin a yanzu akwai rumfunan zabe 176,846 a fadin Najeriya.
INEC na ci gaba da damarar tunkarar manyan zabuka da za a gudanar a 2023.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranakun da za ta gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Ekiti da Osun dake sashin kudu maso kudancin Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ya bayyana a Abuja ranar Laraba cewa za a gudanar da zaben a Ekiti a ranar 18 ga Yuli, 2022, yayin da na Osun za a gudanar a 16 ga Yuli, 2022.
A wani labarin, hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa (INEC) ta bayyana cewa ta soke wasu runfunan za?e 746 dake fa?in Najeriya, wa?anda mafi yawancin su a wurin bauta, gidan sarauta da kuma wuri mai zaman kanshi suke.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya fa?i haka ranar Laraba a Abuja, a wurin taron da hukumar ke gudanarwa da kwamishinonin za?e.
Daga runfunan za?en 119, 973 da ake da su, Farfesa Yakubu yace yanzun akwai runfunan za?e 176, 846 a fa?in Najeriya.