Hukumar DSS Ta Gayyaci Dakta Ahmad Gumi


Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci babban malamin addinin Musuluncin nan dake Kaduna Sheikh Dr Ahmad Gumi zuwa ofishinta biyo bayan wasu kalaman da suka zama sa- in-sa tsakanin Shehin malamin da rundunar sojojin Najeriya.

Wannan ce-ce-ku-ce dai ya biyo bayan wata zantawa da Dr. Ahmad Gumi ya yi da Gidan Talbijin mai zaman kansa na Arise, inda sojojin suka ce malamin ya zargi jami’anta da hada baki da ‘yan bindiga dadi.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Najeriya Brigadier General Onyeama Nwachukwu ya sanyawa hanu na mai cewa zargin da Dr. Gumi​ ya yi wa sojojin Najeriyar fa babbar magana ce, domin ba kawai abin bakin ciki ba ne kawai, amma wani yunkuri ne irin na ganganci don shafawa dakarun bakin fenti ba tare da la’akari da yadda suke sayar da ransu ba don wanzar da tsaro a Najeriya.

Janaral Nwachukwu ya ce wadannan sojojin fa da ake zargi su ne suka sai da ransu wajen ceto daliban kwalejin gwamnatin tarayya ta Yauri da ‘yan bindigar suka sace a kwanannan.

Rundunar sojin Najeriyar ta ce yayin da ba za ta taba bada wani uzuri ga duk wani baragurbi dake cikinta ba, amma kuma dole a fayyace karara ba za ta kuma taba yarda da duk wani zagon kasa ko hada baki koma taimakon abokan gaba daga jami’anta ba.

Sojojin Najeriyar suka ce yayin da suke maraba lale da duk wani suka mai ma’ana a hannu daya kuma ba za su amince da duk kalaman da ka iya karfafa ‘yan ta’adda ba.

Da yake maida martani Dr. Ahmad Gumi​ ya yi watsi da zarge-zargen da rundunar sojin ta yi masa inda mai magana da yawunsa Mallam Tukur Mamu ya ce abubuwan da ke faruwa yanzu abin takaici ne.

Ya ce cikin zantawr da Dr. Gumi​ ya yi, babu inda ya yi ikirari akan sojoji baki dayansu, Mallam Tukur Mamu ya ce abin da malamin ya fada kusan kowa ma na fada don hatta su sojojin su ma da kansu sun sha fada cewa ba za a rasa baragurbi ba a cikinsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply