Hidimar Jama’a Muke Yi A Majalisa Ba Neman Ku?i Ba – Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce ‘yan majalisar dattawa aikin jama’a da hidimtawa kasa suke yi ba wai kansu suke yi wa aiki ba, kamar yadda akasarin jama’a ke zato ko hasashe.

Sanata Lawan ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wani taro a majalisar ranar Laraba, ya ce ‘yan majalisar dattawa suna sane da abubuwan da suke yi.

A cewarsa, ‘yan majalisar sune wadanda suke kusa da jama’a kuma aka fi saukin zuwa garesu cikin wadanda aka zaba.

“Wajibi ne a yi zaben gaskiya da gaskiya a 2023, kuma dole mu mayar da hankali. Idan kun gano wani abu wanda ya dace a yi, ku taimaka ku sanar damu. Kada ku dinga jira mu yi kuskure, sai ku fara fallasawa, kuna cewa wadannan aljihunsu kawai suke gyarawa”.

“Daga ?an zaman da na yi na shugabancin Majalisa, na fahimci cewa ‘yan majalisar nan ba kansu suke yi wa aiki ba. Kuma wannan majalisar tana daya daga cikin wuraren da suka fi taka tsan-tsan.
“Duk abinda za mu yi sai mun bayyana shi, sannan an fi samun damar zuwa wurinmu,”

“Mutane za su iya sukarmu, ko kuma zarginmu da yin yadda muka ga dama. Amma muna yin iyakar kokarinmu tsakanin mu da Allah, kuma Allah shine shaidarmu akan haka”.

Related posts

Leave a Comment