HEPATITIS: Sama Da Mutane Miliyan Biyu Na Ɗauke Da Cutar Najeriya

A taron wayar da kan mutane kan cutar Hepatitis da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta shiry, ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa mutum sama da miliyan 20 na dauke da cutar Hepatitis a Najeriya.

Minista Ehanire ya ce cutar Hepatitis B da C ta yi tsanani a Najeriya yanzu.

Ya ce ma’aikatar lafiya ta gano haka a binciken da ta gudanar a shekarar bara domin sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cututtukan kanjamau da Hepatitis a Najeriya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Kashi 8.1 na dauke da cutar hepatitis B sannan Kashi 1.1 na dauke da Hepatitis C.

Duk shekara WHO na gudanar da taro irin haka domin wayar da kan mutane game da cutar Hepatitis.

Taken taron na bana shine ‘Tsara hanyoyin kare mata da jarirai daga kamuwa da cutar da wayar da kan mutane game da cutar a wannan lokaci da ake fama da annobar Korona’.

Rigakafi cutar

Minista Ehanire ya ce gwamnatin Najeriya na yi wa jarirai allurar rigakafin cutar da zaran an haife su.

Ya ce wata haka hanya ce da zai taimaka wajen dakile samun sabbin wadanda ke dauke da cutar..

Burin gwamnati shine rage yaduwar cutar zuwa kashi 2 a yara a zuwa karshen 2020.

Sai dai wani gudu ba hanzari ba Minista Ehanire ya ce gwamnati na fama da karancin kudade da ake bukata wajen shigo da wadannan magunguna.

Ya ce duk da wannan matsala da gwamnati ke fama da shi an ware dala biliyan 3 domin inganta shigo da magunguna sanan da inganta aiyukan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da zai taimaka wajen yi wa jarirai rigakafin cutar tun daga shekarar 2018 zuwa 2028.

Gwaji da wayar da Kan mutane

Jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO a Najeriya Walter Mulombo ya ce ya zama dole a rika wayar wa da mutane kai game da cutar sannan da hanyoyin da za su kiyaye domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen karfafa gwiwowin mutane su rika yin gwajin cutar da yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafin cutar hepatitis B.

Mulombo ya jinjina wa Gwamnatin Najeriya cewa itace kasa ta 13 a Afrika da suka shirya tsarin yi wa jarirai allurar rigakafin cutar a lokacin da aka haife su.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da cutar gaba daya a kasan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply