Sanarwar da fadar shugaban ?asar ta fitar mai ?auke da sa hannun mai taimaka wa Buhari kan ya?a labarai Malam garba Shehu ta ce, tafiyar na nuna muhimmancin da ke akwai na tsaro da zaman lafiyar Laberiya da sauran ?asashen Afirka ta Yamma.
Bulaguron na Shugaba Buhari ya zo daidai ne da ranar da Laberiya ke bikin murnar shekara 175 da samun ?ancin kanta.
Shugaba Buhari ne babban ba?o na musamman a bikin har ma zai gabatar da jawabi.
Sanarwar ta ce bulaguron na Laberiya na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun matsaloli na rushewar dimokr?aiyya da juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.
A shekara mai zuwa ta 2023 ne za a gudanar da za?uka a Najeriya da Laberiya da kuma Saliyo, kuma ana sa ran Shugaba Buhari zai yi wa ?an Laberiya jawabi kan muhimmancin sahihin za?e marra magudi.
Kazalika fadar shugaban Najeriyar ta ce, Buhari zai jaddada wa ?an ?asar muhimmancin girmama dokar ?asa a baki ?ayan yankin.
“Idan ba a bin dokar ?asa, ba za asamu tsaro da zaman lafiya da ci gaba ba,” in ji sanarwar.
Sa?on Buhari na tafiyar ya ce zaman lafiya da tsaron Laberiya da Saliyo na da muhimmanci ga Najeriya.