Wani jirgin saman rundunar sojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ?asar, bayan da ?an fashi suka bu?e masa wuta.
Jirgin yana komawa ne bayan da ya kammala wani aiki mai cike da nasara a tsakanin iyakokin jihohin Zamfara da Kaduna.
Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar ranar Litinin ta ce sai dai cikin sa’a matukin jirgin Laftanal Abayomi Dairo, ya fita daga cikinsa.
Bayan da ya tsira daga fa?uwa daga jirgin sai kuma ?an bindigar suka bu?e masa wuta, amma ya samu sa’ar kauce musu ya kuma nemi mafaka a wani ?auye har zuwa wayewar gari.
“Daga nan sai ya yi amfani da wayarsa don gano hanyar da za ta fid da shi, inda ya yi sa’ar kauce wa sansanonin ?an bindigar da dama har ya isa ga wani sashe na rundunar sojin Najeriya, inda daga nan ne ya samu tsira,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ?ara da cewa a lokacin da aka samu labarin hatsarin, sai Shugaban Rundunar Sojin Sama Air Marshal Oladayo Amao, ya bayar da umarnin cewa a yi duk ?o?arin da za a yi don ceton matu?in.
“Daga nan ne sai aka yi amfani da hanyoyin le?en asiri na rundunar sojin saman da helikwaftocin ya?i da kuma taimakon rundunar sojin ?asa inda aka gano wajen da hatsarin ya faru tare da ganin lemar da matu?in ya yi amfani da ita wajen sau?a.
Sai kuma suka ci gaba da neman matu?in a kusa da inda lamarin ya faru.
“Abin jin da?i ne matu?a yadda Laftanal Dairo ya tabbatar da cewa shawagin jiragen ya?in a wannan yanki da hatsarin ya faru ya taimaka wajen tsorata ?an bindigar da suke neman gano shi.
“Hakan ce ta sa ya tsere musu har ya samu mafaka,” a cewar sanarwar.
Rundunar sojin sama ta ce mako biyu kenan tun sanda ta fara kai samame ta sama ba dare ba rana a ma?oyar ?an bidniga, don bin umarnin da Shugaba Buhari ya bayar cewa a za?ulo su duk inda suke a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara.