Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Masarautar Katsina ta dakatar da da Hakimin Garin Kankara, Abubakar Yusuf, kan zargin hada baki da ‘yan bindiga da suka addabi al’ummarsa.
Kakakin majalisar Sarki, Iro Bindawa, a ranar Asabar ya bayyana cewa an dakatar da Hakimin ne bisa korafe-korafen mazauna gari da kuma binciken jami’an tsaro.
Kakakin ya kara da cewa an dakatar da shi ne domin taimakawa gwamnati wajen kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a fadin Jihar.
Majalisar ta kaddamar da kwamiti don binciken Hakimin bisa zarge-zargen da ake masa na taimakawa ‘yan bindigan da suka addabi jama’arsa.
Ire-iren haka suna faru a jihar Katsina inda akayi zargin Sarakunan gargajiya da hada kai da ‘yan bindiga wajen cutar da al’ummarsu.