Harin Zulum: Alama Ce Ta Rayuwarmu Na Cikin Hatsari – Gwamnoni

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ta ce farmakin da gungun maharan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a garin Baga, alama ce dake nuna cewar su kansu gwamnoni basu tsira daga barazanar kungiyar ta Boko Haram ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya fitar da sanarwar hadin gwiwar ga manema labarai, bayan taron da suka yi a ranar litinin a Abuja.

Taron gwamnonin da ya maida hankali kan sha’anin tsaro, ya koka kan yadda lamurra ke kara tabarbarewa a sassan Najeriya, duk da kokarin gwamnati na kawo karshen matsalar.

Ranar lahadin nan da ta gabata yayin karbar bakuncin gwamnonin Jigawa da Kebbi a Maiduguri, gwamna Babagana Zulum ya jadadda cewar, akwai wadanda ke yiwa gwamnati zagon kasa ga kokarinta na murkushe ta’addanci, matsalar da yace ba za ta bari a kawo karshen matsalar da yankin arewa maso gabshin kasar ke ciki ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply