Hedikwatar tsaro a Najeriya ta lashi takobin lalubo ƴan bindigar da suka kashe tare da sace wasu jami’an sojoji bayan wani hari da suka kaddamar a makantar soji ta NDA a Kaduna.
Wasu mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda ɗaya yayin harin da suka kai ranar Litinin da tsakar dare.
Sanarwar da shugaban hafsoshin sojin Najeriya Janar Lucky Irabor ya fitar, ta mika sakon ta’azziya ga iyalan sojojin da aka kashe, sannan ya shaida cewa an sake inganta tsaro a makarantar da kewayenta.
Sannan ya ce yanzu haka an bazama a wani samamen haɗin-gwiwa domin ceto sojan da aka sace da kuma kama ƴan bindigar.
Sanarwar ta kuma shaida cewa nan gaba za a sake fito da wasu bayanai kan halin da ake ciki.
Masu sharhi kan lamuran tsaro dai na ganin harin a matsayin wani abin kunya ga sojoji wadanda a baya, duk karfin halin dan bindiga, ba zai daddara ya kai musu hari ba.