Harin Kwantan ?auna: Boko Haram Sun Hallaka Sojoji 20

Akalla Sojojin Najeriya Ashirin (20) sun rasa rayukansu yayinda saura da dama suka jikkata yayinda wasu yan ta’addan Boko Haram suka kai harin kwantan bauna jihar Borno ranar Talata.

An ruwaito cewa harin ya auku ne a hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ana saura kimanin kilomita 30 da garin Damboa.

Majiya daga gidan Soja ta labarta cewa ‘yan ta’addan sun budewa Sojoji wuta ne kuma hakan yayi sanadiyar mutuwar Soji da dama.

Yace: “Abin da ban takaici, Dakarunmu sun je sintiri kuma yayinda dawowansu Damboa, kimanin kilomita 30, sai ‘yan ta’addan suka bude musu wuta ta ko wani hanya.”

“Mun yi asaran fiye da Sojoji dozin.”

“An kai gawawwakin Sojin da suka mutu Maiduguri tare da wadanda suka jikkata.”
“Yanzu haka suna jinya a wani asibitin Sojoji,”

Anata ?angaren rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa, a wani kicibus da ta yi da mayakan Boko Haram a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, ‘yan ta’adda 17 sun bakunci lahira.

Haka zalika ta sanar da cewa, wasu da dama daga cikin ‘yan kungiyar masu tayar da kayar bayan sun tsere da raunuka daban-daban na harbin harsashi.

A yayin jaddada gagarumar nasarar da dakarun sojin suka samu yayin wannan artabu a ranar Talata, an kuma tsinto miyagun makamai da mayakan suka zubar yayin neman ta kansu.

Da ya ke karar kwana babu inda ba ta kai ziyara, rundunar sojin kasan ta yi rashin sa’a yayin da wasu dakaru biyu suka sadaukar da rayukansu wajen kare martabar kasar nan.

Haka kuma wasu dakarun hudu sun jikkata yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram a filin daga.

Related posts

Leave a Comment