Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Jagoran ‘yan ta’addan da suka sace Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya ce gwamnatin tarayya na da zaɓi biyu, ko dai ta saurari fasinjojin ko ta mance babin su.
Jagoran ‘Yan ta’addan, wanda ya rufe fuskarsa, ya faɗi hakane a wani sabon Bidiyo, wanda ya nuna nutum 8 daga cikin fasinjojin na rokon gwamnatin tarayya ta kawo musu ɗauki.
Mutumin wanda ya yi magana cikin harshen turanci, ya ce: “Mune mutanen da suka sace Fasinjoji daga jirgin ƙasar Kaduna-Abuja, suna ta rokon mu da cewa suna bukatar mu ba su dama su yi magana da gwamnatin tarayya.”
“Saboda haka yanzu mun ba su dama su yi magana, daga nan ya rage gare ku, ku saurare su ko kuma ku mance da su.”
Ɗaya daga cikin mutanen da ke hannun yan ta’addan wacce ta bayyana sunanta da Mariam Abubakar, ta ce ‘ya’yanta sun kamu da rashin lafiya a sansanin yan bindiga.
“Ina daga cikin fasinjojin da aka sace a jirgin ƙasa tare da iyalaina hudu da kuma Mijina, muna rokon gwamnatin tarayya, yan uwan mu da duk wanda yake tausaya mana su kawo mana agaji.”
“Mun kwashe kwanaki 62 a wurin nan, mun kwanta rashin lafiya, biyu daga cikin ƴaƴana ba su da lafiya tare da babu mai kula da lafiyarsu. Saboda haka muna rokon ku kawo mana ɗauki.”
Iyalan Fasinjojin da aka sace sun jima suna kiran gwamnatin tarayya ta kuɓutar da yan uwansu, yayin da a bangarenta Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa tana ɗaukar matakan da ya dace na kuɓutar da su.