Harin Borno: Boko Haram Sun Hallaka Mutane 30

Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu a harin da ‘yan ta’addan da ake kyautata zato ‘yan kungiyar ISWAP ne suka kaiwa tawagar jami’an gwamnatin jihar Borno yayinda suke hanyar zuwa Baga.

Majiyoyi biyu sun bayyanawa AFP ranar Asabar cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya ninku daga Juma’a zuwa yau saboda an tsinci wasu gawawwaki.

Wadanda aka kashe sun hada da ‘yan sanda goma sha biyu, Sojoji biyar, ‘yan sa kai hudu da fararen hula tara.

Harin ranar Juma’a ne karo na biyu da aka kaiwa gwamnan cikin watanni biyu. A cewar majiyoyin da ke da masaniya game da harin, sun bayyana cewa jami’an gwamnatin sun nufi Baga ne cikin shirin da gwamnatin jihar keyi na mayar da masu gudun hijra gidajensu daga Maiduguri.

Rundunar Sojoji, ‘yan sanda, da ‘yan sa kai suna tare da su domin tabbatar da tsaro a hanyar.

‘Yan Boko Haram sun bude musu wuta ne a wani wuri mai suna Korochara, kimanin kilomita 2 zuwa barikin Sojojin hadaka MNJTF Baga.

Majiyar Premium Times ta bayyana cewa an kai harin ne misalin karfe 2 na rana. Shi gwamnan Borno tuni ya tafi cikin jirgi mai saukar angulu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply