Hari Kan Jirgin Abuja-Kaduna Ya Tayar Da Hankula

Rahotannin dake shigo mana daga sassa daban-daban na kasar nan na bayyana cewar harin da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin ?asan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da daddare ya ?aga hankulan ?an Najeriya tare da sanya fargaba a zu?atan mutane da dama.

Al’amarin ya jawo asarar rayuka da har yanzu hukumomi ba su fadi yawansu ba, sannan wasu sun jikkata sakamakon bu?e wuta da maharan suka yi bayan da jirgin ya taka bam din da suka dasa a kan hanyarsa.

Wannan batu ya zama matsalar tsaro ta baya-bayan nan mafi muni da ta faru a ?asar da kuma ta ?imauta mutane, musamman ganin akwai a ?alla fasinjoji 970 a cikin jirgin.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama jigo mai sada miliyoyin mutane da arewacin ?asar daga babban birnin tarayya Abuja da kuma kudanci.

Hakan ne ya sa mutane suka fi raja’a da bin jirgin ?asan ganin yadda ya zama wata hanyar sufuri da mutane suke ganin ita ce mafi tsaro, fiye da bin hanyar mota, yayin da jirgi kuma ya yi tsadar da sai masu ido da kwalli ne za su iya biya.

A shafin tuwita an yi ta musayar ra’ayoyi inda aka yi amfani da maudu’an #Nigeria da #Kaduna sau kusan 100,000, a Facebook kuma a kalla sama da mutum 68,000 ne suka tattauna kan batun.

Tuni dai gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya kai ziyara asibiti don duba majinyatan, sannan kuma mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ma ya je jaje Kadunan

Related posts

Leave a Comment