Hare Haren ‘Yan Bindiga Na Kara Kamari A Birnin Tarayya Abuja

IMG 20240405 WA0020

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Gaba da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja.

Bisa ga binciken da aka yi, ‘yan bindigar da yawansu ya haura shida, sun shiga kauyen ne da misalin karfe 12:15 na tsakar dare wayewar garin Laraba.

Maharan sun halaka mutum ɗaya yayin harin, kuma suka yi awon gaba da wasu mutum biyu, tare da jikkata wasu da dama.

Wani jami’in gwamnati, wanda ke zaune a unguwar ya shaida wa ƴan jarida cewa an yi garkuwa da mutum biyu sannan aka kashe daya a harin.

Wata majiya mai karfi a cikin rundunar ‘yan sanda, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce dakarun ‘yan sanda na nan suna farautar ‘yan bindigan da suka kai harin.

Ya koka game da ƙaruwar masu kai wa ƴan bindiga bayanan sirri, yana mai ƙara wa da cewa matsalar infomomi babban abin damuwa ce.

Duk kokarin jin ta bakin jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh ya ci tura domin ba ta ɗaga kira ko amsa sakonnin da aka aike mata ba.

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply