Hare Haren ‘Yan Bindiga: Gwamnan Katsina Ya Nemi Agajin Gwamnatin Tarayya

IMG 20240211 WA0197

Gwamnan jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tallafa wa kokarin da jihar take yi wajen yaki da ‘yan bindiga.

Gwamnan ya yi wannan roko ne a lokacin da yake jawabi ga matasan ƙauyen Wurma da suka yi zanga-zangar adawa da munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa yankin.

Yayin wannan ziyara da ya kai domin rarrashin masu zanga-zangar, Gwamna Raɗɗa ya jajantawa iyalan waɗanda hare-haren ya shafa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply