Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa haramta wa wasu ‘yan Najeriya shiga Amurka da Shugaba Trump yayi a kan aikata magudin zaben da suka tafka a jihohin Kogi da Bayelsa.
PDP ta sanar da hakan ne a wata takardar da sakataren jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, Kakakin jam’iyyar ya sake bukatar cewa a kara saka takunkumin hana visa a kan iyalan wadanda aka hana Bayan saka wa wasu ‘yan Najeriya takunkumin hana visa sakamakon tafka magudin zaben da suka yi.
Babbar jam’iyyar adawar a wata takarda da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam’iyyar ya saka hannu a ranar Talata, 15 ga watan Satumba, ya ce masu magudin zaben suna zagon kasa ga damakoradiyya.
Jam’iyyar PDP ta kara da bukatar kasar Amurka da ta kara takunkumin a kan iyalan wadanda suka tafka magudin zaben. A yayin ci gaba da bayani, Ologbondiiyan ya bukaci da a kwace kadarorin wadannan makiyan damokaradiyyan saboda hakan ya zama izina ga sauran masu son aikata abinda suka yi.
PDP ta kara da cewa, idan har aka hana ‘yan siyasa shiga sauran kasashen duniya, hakan zai zama babban jan kunne ga shugabannin APC domin su kiyaye tsaro da magudi a yayin zabe.