Harajin Filin Idi: El Rufa’i Ya Yi Amai Ya Lashe

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ?ar?ashin jagorancin Nasiru El Rufa’i ta janye matakinta na karbar harajin N500, 000 kafin bayar da izinin amfani da dandalin wasanni na Murtala domin gudanar da Sallar Idi.

Batun ya tayar da jijiyoyin wuya bayan da ‘yan kwamitin masallacin Kano Road, wadanda ke amfani da filin wajen gudanar da sallar a duk shekara, sun bayyana mamakinsu kan matakin ganin cewa sun kwashe shekara da shekaru suna sallar Idi a cikinsa ba tare da bayar da ko sisi ba.

Daya daga cikin mambobin kwamitin, Malam Sabi’u Garba, ya shaida wa BBC cewa ba su ji dadin harajin da gwamnati ta sanya musu na amfani da filin ba.

“Wannan wani abu ne da ba mu taba jin sa ba, a ce mutum zai yi sallah sai ka biya kudin ibadar da za ka yi a arewacin Najeriya. Wannan wuri da muke sallah, Sardauna ma a nan ya rika sallah…iyayenmu da kakaninmu sun tabbatar da cewa an ba su takardun izinin (amfani da wurin don yin sallar Idi),” in ji shi.

3- 2023: Ana Amfani Da Addini Wajen Raba Kan Jama’a – Dattawan Arewa

Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta nuna fargabar cewa ?abilanci da kwa?ayi na barazanar kawo cikas ga ?o?arin farfadowar kasar a zaben 2023.

Kungiyar ta bayyana damuwa kan abubuwan da ke faruwa a bangarori da dama na siyasar Najeriya dangane da shirye-shiryen zaben 2023.

Wata sanarwa da daraktan Yada Labarai na kungiyar Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya fitar a Abuja, ya zargi wasu ?an siyasa da abun da ya kira ‘’amfani da addini wajen raba kan yan ?asa’’

Related posts

Leave a Comment