Har Yanzu Najeriya Kasa Ce Mai Tasowa – Gwamnatin Tarayya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan kwadago da ayyukan yi na Chris Ngige ya ce a matsayin Najeriya na kasar da ke tasowa a yanzu, ba ta da karfin da za ta iya yin tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da shawara na ko wanne likita ya rika duba marasa lafiya 600.

Mr Ngige ya bayyana haka ne a wani taron kwana biyu da ake yi duk bayan wata uku na kwamishinonin lafiyar Najeriya wanda ya gudana a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa an yi wa wannan taro na kwana biyu lakabi da “kara gina bangaren lafiya a Najeriya ta hanyar hada hannu da abokan hulda”.Quote Message: Ministan ya ce ” ba MDD ce ta mallaki kasarmu ba, kuma yanzu muke tasowa. lokacin da suka gayan wannan dokar ni kuma zan ce musu ko wacce doka na da wanda ake daga wa kafa cikinta. Har yanzu mu ba mu zo wurin ba.

Ministan ya ce ” ba MDD ce ta mallaki kasarmu ba, kuma yanzu muke tasowa. lokacin da suka gayan wannan dokar ni kuma zan ce musu ko wacce doka na da wanda ake daga wa kafa cikinta. Har yanzu mu ba mu zo wurin ba

Labarai Makamanta

Leave a Reply