Har Yanzu Buhari Na Gyaran Ɓarnar Da PDP Ta Yi Ne – APC

Jam’iyya mai mulki ta APC ta bukaci jam’iyyar adawa ta PDP da ta yi shiru ta daina tsoma bakinta a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke aikin gyara barnar da sukayi a kasar.

Shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus a wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, ya bukaci shugaba Buhari da yayi murabus akan kashe kashen da ake yi a kasar.

Ya kuma bukaci Buhari ya yi murabus saboda yawaitar cin hanci da rashawa da ake tafkawa a karkashin gwamntinsa.

Mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya ce babu wanda yake sa ran PDP za ta bada wata shawarar ci gaba la’akari da irin barnar da ta tafka a mulkinta.

Jam’iyyar APC ta ce kiran da PDP ta yi ba zai rasa nasaba da cincirindon masu ficewa daga jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyu ba.

APC ta ce: “Nigeria na bukatar hamayya mai ma’ana ba wai irin hauragiyar da jam’iyyar PDP ke yi da sunan hamayya ba.

“Ba abun laifi bane idan mambobin PDP suka sauka daga jirgin da ke kokarin nutsewa suka hau wanda zai kaisu tudun mun-tsira. Kamar dai karin maganar nan; me zai sa ka tashi sama kamar kaza alhalin zaka iya yin shawagi kamar na hankaka?

“Munji dadi sosai da yadda tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya fice daga PDP ya dawo APC.

“A yayin da muka yi aiki kafada da kafada domin cimma muradun mu na gina Nigeria, mun san dole ne mu fuskanci matsalolin akan wannan gwadabe.

“Sai dai, shi shugaban kasa Muhammadu Buhari jajurtacce ne, tuni dama muka aiwatar da mafi akasarin alkawuran da muka dauka a yayin da muke yakin zabe.

“Mun samu nasara mai yawa a wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa tare da jin dadin rayuwa,” a cewar APC

Labarai Makamanta

Leave a Reply