Sanata mai wakiltar yankin kudancin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ya tabbatar wa BBC batun da Gwamna Zulum ya ambata cewa akwai wasu ƙananan hukumomin jihar da ƴan Boko Haram ke da ƙarfi a can.
Sanatan ya faɗi hakan ne a wata hira a ranar Alhamis, sakamakon rahotannin da aka ambato Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar na cewa har yanzu ƙananan hukumomin Abadam da Guzalama na ƙarƙashin ikon Boko Haram.
Ya ƙara da cewa amma fa Boko Haram ɗin yaƙin sari ka noƙe suke yi. Ba za ka ce ga ƙaramar hukuma taƙamaimai da ke hannunsu ba amma sukan yi gayya ne su je su kai hari.