Har Yanzu Babban Banki Bai Wadatamu Da Sabbin Takardun Naira Ba – Bankuna

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Bankunan kasuwanci a Najeriya sun mayar da martani kan iƙirarin babban bankin Najeriya CBN kan cewa ya bai wa bankunan kasuwanci isassun sababbin kuɗaɗe kawai sun riƙe su ne.

An ruwaito cewa Mrs Hadiza Ambursa wadda jami’a ce a Access Bank, wadda ta wakilci manajan darakta ta ce, an ba su kashi 10 ne kacal cikin 100 na kuɗin da suka bai wa CBN.

A yayin wani zama da wakilan bankunan kasuwanci suka yi da kwamitin majalisar tarayya, ma’aikaciyar ta ce “Ba ma samun kuɗin cikin gaggawa kamar yadda muke buƙata. Muna samun kashi 10 ne kawai cikin 100 na abin da muka kai wa CBN. Muna biya muna kuma karɓa kudi. Kuma a gefe ɗaya muna sanya kuɗin a ATM.

Mista Jimoh Garuba wanda wakilin Sterling Bank ne, yace bankin nasu yana samun kuɗi daga CBN amma ba ya kai wa yadda zai isa ga buƙatun kwastomominsa.

Yace, bankinsu na karɓar abin da bai gaza naira miliyan 150 ba daga CBN kowanne mako su rabawa reshinansu da ke Abuja.

Ya ƙara da cewa a Kaduna, bankinsu ya ƙarbi naira miliyan 150 a kowanne mako ya kuma raba su ga duka rassansa da ke jihohi 36 na tarayya.

Ya ce a Kano, “ana bamu naira miliyan 100 ne a mako, ba za mu iya komau da su ba bayan sanyawa a na’urar ATM”.

Ms Arerepade Akagwe, wadda wakilin United Bank for Africa (UBA) ne, ta ce ta karbi kashi 70 na tsofaffin kuɗin da ta bai wa CBN.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN akwai sauran bankuna irinsu Guarantee Trust Bank (GTB), ECO bank, Lotus Bank da Fidelity da suka amince sun karɓi kimanin kashi 60 na tsafaffin kuɗin da suka mayar wa CBN.

Shugaban kwamitin ɗan majalisar wakilai alhassan Ado-Doguwa ya ce gayyatar da aka yi wa bankunan ba abin ta da jijiyar wuya ba ne, yanayi ne na bincike kan abin da ya shafi al’umar Najeriya.

“Muna da buƙatar sanin gaskiya kan ainihin iƙirarin da bankunan kasuwanci suke yi na cewa CBN bai bayar da sabbin kuɗi ba, da kuma na CBN da ke cewa ya bayar da kudaden da suka kamata.

Labarai Makamanta

Leave a Reply