Har Yanzu Ba Mu Daidaita Da Gwamnati Ba – Malaman Jami’o’i

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ce har yanzu tana nan a kan bakanta, bata dakatar da yajin aikinta ba, saboda gazawar Gwamnatin Tarayya na cika alwashin da ta yi musu na biyan haƙƙoƙi da buƙatun su, kuma lallai zasu cigaba da yajin aiki har illa masha Allahu.

Shugaban kungiyar malaman reshen jihar Legas, Farfesa Olusiji Sowande, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoban 2020, a ganawar su da manema labarai a birnin Ikko.

Sowande ya ce rahotannin kafafen yada labarai da ke ikirarin sun dakatar da yajin aikin ba gaskiya bane. Ya kara da cewa, labaran da ake yadawa na cewa gwamnatin tarayya ta sakar musu kudi har naira biliyan 30 ba gaskiya bane.

Jigo a kungiyar ya yi bayanin cewa tattaunawar da ake yi tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya domin samun sasanci bai kammala ba kuma suna kan hakan ne.

Hakazalika, jigon kungiyar ya ce majalisar zartarwa ta kungiyar malaman jami’o’in ne kadai za ta iya sanar da janye yajin aikin. Ya kara da cewa, hukuncin majalisar zartarwan kuwa dole a kai shi gaban kungiya domin tattaunawa, don haka ba zai yuwu ko shugaban kungiyar ya iya janye yajin aikin ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply