Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Har Yanzu Ba A Tabbatar Da Laifi Akan Kyari Ba – Hukumar ‘Yan Sanda

Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ta ɗauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda DCP Kyari ne biyo bayan shawarar da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli.

“Matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka [FBI] ke yi masa,” a cewar sanarwar.

IGP Usman Alkali ya kafa kwamati na mutum huɗu ƙarƙashin jagorancin DIG Joseph Egbunike wanda zai binciki zargin da ake yi wa Abba Kyari, wanda shi ne shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).

Ana zargin Abba Kyari da karɓar cinhanci a hannun matashi ɗan Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, domin kamawa da kuma muzguna wa wani abokin harkarsa, Kelly Vicente. Sai dai Kyari ya musanta zargin.

Hushpuppy ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar ce yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane.

Sai dai rundunar ta ce har yanzu tana ɗaukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa.

Exit mobile version