Har Abada PDP Ba Za Ta Sake Mulki A Najeriya Ba – Ambasada Ahmad

Tsohon minista tama da karafa, kuma tsohon Jakadan Nijeriya a kasar Turkiya duk a lokacin tsohuwar gwamnatin PDP, Ambasada Ahmad Abdulhamid Mallammadori, ya yi ratsuwa da Allah cewa jam’iyyar PDP ta daina mulki a kasar nan.

Ambasada Ahmad ya baiyana hakan ne a birnin Dutse yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Ambasada Ahmad ya ce duk mawuyacin halin da ake ciki yanzu a Nijeriya jam’iyar PDP ce ta jefa al’ummar kasar nan ciki, kuma a cewar Ambasada Ahmad hakan ma ya zo da sauki domin da jam’iyar PDP ta koma kan mulki, to da yanzu babu Nijeriya.

Daga karshe Ambasada Ahmad ya bukaci al’ummar da su ci gaba da yi wa shugaban kasa addu’ar Allah ya ci gaba da ba shi damar ci gaba da aiyukan alkairi kamar yadda ya fara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply