Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta bayyana irin rawar da marigayi Mallam Isma’il Isa Funtua ya rika taka wa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, wajen kishi da taimakawa jama’a musamman Mata.
Hajiya Aisha a ranar Laraba, ta fayyace yadda Marigayi Mallam Funtua ya jajirce wajen goyon bayan mata masu damawa a harkokin siyasa musamman a tsawon shekaru hudun da suka gabata.
Uwargidan shugaban kasar ta ce Marigayi Funtua ya rika faɗi-tashin ganin an bai wa mata akalar jagoranci a Hukumomi da Cibiyoyi a gwamnatin Buhari.
Aisha Buhari ta bayyana hakan ne cikin wani sakon na alhini kan mutuwar Mallam Funtua da ta wallafa a shafukanta na dandalan sada zumuta.
Mallam Funtua wanda ya kasance aminin shugaban kasa Buhari, ya yi gamo da ajali ne a ranar Litinin a sakamakon bugun zuciya kamar yadda wani makusancinsa ya bayyana.
Aisha Buhari ta ce za a rika tunawa da Funtua saboda goyon bayan da ya rika bai wa mata ‘yan siyasa wajen ganin sun rike madafun iko. “Inna lillahi Wa inna ilaihi Raji’un; ma’ana daga Allah muke, kuma gare shi zamu koma.” “A madadin dukkanin iyalina, ina mika sakon ta’aziya ga Hajiya Hauwa Isa Funtuwa da duk iyalinsa Marigayi Mallam Isma’ila Isa Funtua ta wannan babban rashi da suka yi.
” Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya sa Aljannatul Firdausi makomarsa.” “Ba za a manta da Mallam Isma’ila Isa Funtua saboda goyon bayan mata ‘yan siyasa musamman rawar da ya taka wajen ganin sun samu naɗin mukamai a Hukumomi daban-daban tsawon shekaru hudu da suka gabata.