Har Abada APC Ce Za Ta Cigaba Da Mulkin Najeriya – Ɗanlami

Kwamishinan Wasanni da Walwalar Al’umma na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliiyu Danlami ya bayyana cewa da yardar Allah wata jam’iyya ta gama yin mulki a kowane mataki, in ba jam’iyyar APC ba, saboda yadda ta jajirce na ganin ta tallafawa al’umma, kuma tallafi ya samu Isa wajen su kai tsaye, musamman a wajen iyayen mu mata, kuma tallafin yana zuwa dagaa matakin gwamnati tarayya da na jiha.

Sani Danlami ya bayyana haka a lokacin da ake kaddamar da shugabanni riko na jam’iyyar APC a mataki karamar hukumar Katsina, a jiya talata.

Sani Danlami, kuma Garkuwan Arewan Katsina ya kara da cewa kowa ya sani, irin gagarumar ci gabada da gwarzon kuma hazikin gwamna, Aminu Bello Masari da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari na ganin an tallafawa al’umma musamman masu karamin karfi. Haka kuma, masu rike da jam’iyyar su kara shiga lungu da sakon domin kara wayar da kan al’umma, don ganin an kara fiddo ayyukan alheri da mai girma Gwamnan Jihar Katsina ke yi a wannan jiha ta mu, da ayyukan alheri da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ke yi a kasar nan. Kowa ya sani an yi gwamnatocin da suka gabata, amma idan ka waiwaya a wajen iyayen mu Mata, ba’a taba gwamnati da ta ba da tallafi ba ya ke zuwa kai tsaye wajen talakkawa ba, kamar a gwamnatin APC ba.

Kwamishinan Wasanni da Walwalar Al’umma, Alhaji Sani Aliiyu Danlami, wanda tsohan danmajalisar tarayya ne, da ya wakilci karamar hukumar Katsina, ya ci gaba da cewa halin da kasar nan take ciki da kuma jihar Katsina ke ciki na matsalar rashin tsaron, mun gaje shi daga gwamnatin da ta shude, wadda idan Allah ya yarda sun gama mulki, a Nijeriya da jihar Katsina, ko’ina maganar ci gaban da jam’iyyar APC ta kawo ake. Ya zama wajibi mu cigaba da addu’o’in ba dare ba rana, don ganin Allah ubangiji ya zaunar da kasar nan da jihar Katsina lafiya.

Daga karshe ya yi wa, shugabanni addu’a da fatan alheri da kuma su ci gaba da jajircewa da cigaba da kula da jam’iyyar APC ba dare ba rana na yada manufofin jam’iyyar APC.

Labarai Makamanta

Leave a Reply