Hanyoyi 50 Da Ake Gane ‘Yan Ma?igo – Sister Bilkisu Ahmad

1- Macen da take bayyanawa ‘yar uwarta mace tsiraicinta.

2- Macen da ke yaba kyawun ‘yar uwarta mace ta fuskar sha’awa.

3- Macen da ke rungumar ‘yar uwarta mace ko sumbatarta da nufin wasa.

4- Macen da take nunawa kawarta bidiyon ‘yan madigo.

5- Macen da za ta kama hannun mace ‘yar uwarta ta dinga shafawa babu wani dalili.

6-Ko Macen da za ta dinga shafa gashin kan kawarta.

7- Mace mai lazimtar kwanciya kan cinyar mace ‘yar uwarta ba tare da dalili ba.

8- Macen da a kodayaushe take son ganin surar jikin mace ‘yar uwarta.

9- ‘Yar madigo tana da yawan son yin kyauta ta bajinta da ban mamaki ga wadda ta gani tana so.

10- Yana daga cikin alamomin ‘yan madigo kebancewa kuryar daki su kadai.

11- ‘Yar madigo ba ta da wata hira sai ta mace ‘yar uwarta.

12- Suna kyamatar yin mu’amala da namiji, ba su damu da yin saurayi ba.

13- Suna da sha’awar kallon fina-finan batsa, musamman na ‘yan madigo.

14- Suna matukar zama a gidan da mata ne zalla, kamar zawarawa da ‘yan mata.

15- Macen da ke tube rigarta a gaban mata ‘yan uwanta ba tare da jin kunya ba.

16- Mace mai yawan son shafa nono ko taba mazaunan kawarta maimakon musabaha.

17- Suna yawan kiran junansu da ‘Sweety’ ko ‘Darling’ ko ‘Dear’ ko kuma ‘My Love’.

18- Suna da son yin dinki matsattse mai bayyana dukkan surar jikinsu.

19- Sun iya yin fari da idanu don janyo hankalin macen da suke so.

20- Sun fi ko?a kyawun mace fiye da namiji
Suna da bakin kishi.

21- Suna da son yin tsabta ta kece raini.

22- Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka.

23- Suna son saka sarka a kafarsu da zobe a yatsan kafar (Duk da an mayar da shi ado yanzu).

24- Suna son saka zobe a babban dan yatsan su na hannu.

25- Yawancin su suna son kara tsawon gashin idonsu ko shafa masa kala.

26- Suna auren junansu kamar yadda namiji ke auren ‘ya mace.

27- Shakuwa mai tsanani tsakanin mace da mace, barci kawai ke raba su.

28- Mace ta mayar da gidan kawarta kamar wurin aikin ta, kodayaushe tana zuwa gidan.

29- Suna ba junan su abinci a baki kamar yadda mata da miji ke yi.

30- Suna tausasa lafazinsu yayin amsa wayar wadda suke harka tare ko suke so.

31- Sukan biya wa junansu bukata ta hanyar kiran waya ko hira a kafar sada zumunta.

32- Ana gane su ta hanyar hotunan mata da suke ajiyewa a wayoyin su.

33- Suna kulla mummunar gaba ga duk macen da take nema ta yi musu kwacen kawa.

34- Suna yawan daga gira ko yin kifce wajen nunawa ‘yar uwarsu wadda ta kwanta a ransu.

35- Suna da yaren da suke yi a wajen hirarrakin su, ta hanyar kushewa ko yaba junansu.

36- Masu auren cikinsu suna yawan tafiye-tafiye da mu’amala da manyan mata.

37- Ba sa gamsuwa da ?a namiji sai sun ayyana yadda suke saduwa da abokiyar harkarsu.

38- Suna tsanar aure duk sanda aka yi musu maganar shi.

39- Suna da kalaman gane juna, irin ‘Muna tare’, ‘Kin tayar min da tsumi’, ‘Za ki yi dadin harka’.

40- Suna son amfani da kwayoyin da za su fitar da cikon halittarsu, kamar kirjinsu da mazauni.

41- Yawancin masu auren cikin su ba sa son haihuwa.

42- Mace ‘yar madigo tana nesanta kanta ga kalaman batsa ga namiji, kuma tana kame kanta.

43- A kafafen sada zumunci suna dora hoton kafa, harshe ko kuma leben mace da sauransu.

44- Suna sha’awar saka dankunne ko wata sarka a hancinsu (Duk da an mayar da shi ado).

45- Ba su damu da kulawa da kuma nuna kishin mazajen su ba.

46- Idan suna kallon fina-finan turawa sun fi mayar da hankali kan matan.

47- ‘Yar madigo ba ta sanya kumbar kanti, kuma ba ta barinta ta yi tsayi a ‘yan yatsunta.

49- Wasun su suna rage gashin kan su kamar na maza kuma suna sa masa kala.

50-Suna yin zanen tatoo mai kusurwa uku (triangle) a hannu ko kafarsu.

Related posts

Leave a Comment