Hangen Nesa: Buhari Ya Kafa Kwamitin Bunƙasa Najeriya A Shekaru 30 Masu Zuwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin bunƙasa ƙasa nan da shekara 30 masu zuwa mai suna Agenda 2050, ƙarƙashin jagorancin dan kasuwar nan Atedo Peterside dan garin Port Harcourt kuma mamallakin Stanbic Bank da kuma ministar kudi da kasafi da tsare-tsare ta kasa Zainab Ahmed.

Ana sa ran wannan muradin na Nijeriya na 2050 zai cire ‘yan kasar mutum miliyan 100 daga talauci sakamakon hasashen da Bankin Duniya ya yi na cewa nan da zuwa shekarar 2040 adadin ‘yan Nijeriya zai kai kimanin mutane miliyan 400.

Kwamitin zai gaji shirin Nijeriya ne na Vision 2020 wanda gwamnatin marigayi Umar Musa Yar’adua ta ƙaddamar a 2009, da kuma shirin ERGP (Economic Recovery and Growth Plan) da aka kafa 2017 domin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.

Kwamitin da gwamnatin ta kafa zai ƙunshi gwamnoni shida, daya daga cikin kowane yanki na ƙasar, da kuma ‘yan majalisa da sanatoci da ministoci da wakilan hukumomi da na manyan jam’iyyu, da ‘yan kasuwa da ‘yan jarida da dai sauransu.

Me za ku ce?

Labarai Makamanta