Hajjin Bana: Yau Alhamis Mahajjata Ke Hawan Arfah

Yau Alhamis 30 ga watan Yulin shekara ta 2020 wacce ta yi daidai da 09 ga watan Dhul-Hajji, ta kasance ranar da Mahajjata ke hawa Arfah a ƙasa mai tsarki wato Saudiyya.

Sai dai a bana Mahajjatan sun kasance ‘yan ƙalilan ne wato adadin da Hukumar kasar Saudiyya ta amince da shi a bana mutane dubu goma, domin kariya daga iftila’in cutar nan ta Covid-19 da aka fi sani da suna CORONA.

Hawan Arfah dai wani babban rukuni ne daga cikin rukunan aikin Hajji, malaman addinin Musulunci sun yi ittifaƙi akan cewar duk wanda ya rasa wannan rukunin to babu shakka ya rasa aikin Hajjin shi.

Ya tabbata a cikin hadisai na Manzon Allah SAW cewa a wannan rana ta Arfah ana bukatar sauran Musulmi wadanda ba Mahajjata ba da ɗaukar azumi, inda aka bayyana cewar yin wannan azumi yana da falala mai tarin yawa.

A baya dai a irin wannan rana ta hawan arfa 09 ga watan Dhul-Hajji kimanin musulmi miliyan uku ne ke tsayuwar shi, amma a bana mutane dubu goma ne kacal zasu yi tsayuwar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply