Hajjin Bana: Saudiyya Ta Tsayar Da Ranar Hawan Arafa

Hukumomin Saudiya sun bayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuli a matsayin ranar hawa Arafa, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Zul Hajji a yau Litinin, abin da ke nuna cewar gobe watan Zul Kida zai cika 30.

Kotun Kolin Saudiya ta ce ranar Laraba mai zuwa za ta zama ranar 1 ga watan Zul Hijja saboda cikar watan Zul Kida, abin da ya sa za a hau Arafat ranar Alhamis 30 ga watan Yuli.

A karkashin wannan tsari, ranar Juma’a 31 ga watan Yuli ta kasance ranar babbar Sallah ko kuma Eid-el Adha.

Kimanin mutane dubu 1 ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar coronavirus wadda ta tilasta wa mahukuntan Saudiya daukar matakin rage yawan mahajjata daga sassan duniya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply