Masarautar Saudiyya ta umarci maniyyata da su yi allurar rigakafin COVID-19 gabanin aikin Hajjin na 2021, in ji jaridar Okaz.
Masarautar ta bakin Ministan Kiwon Lafiya, Tawfiq al-Rabiah, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin din da ta gabata, Aljazeera ta ruwaito.
Ministan ya ce “Alurar rigakafin ta COVID-19 wajibi ne ga wadanda suke son zuwa aikin Hajji kuma zai kasance daya daga cikin manyan sharudda (na karbar izinin zuwa).”
Aikin Hajji shiri ne na hajji wanda ke maraba da miliyoyin Musulmai a duk fa?in duniya wadanda yawanci sukan ziyarci Ka’aba, “Dakin Allah” a cikin garin Makka mai alfarma, a Masarautar Saudiyya.
Har ila yau, shirin ya kasance wani karin hanyar samun kudin shiga ga kasar ta Gabas ta Tsakiya mai arzikin mai.
A shekarar 2019, shirin aikin hajji ya samu sama da baki miliyan biyu a duk fadin duniya. Aikin hajji, duk da haka, ya sami babbar matsala a shekarar 2020 saboda bullowar COVID-19 kamar yadda ibadar ta kasance iyakance ga mutane 10,000 kadai.
Mummunar cutar ta kashe sama da mutane miliyan biyu a duniya kuma ta kuma harbu ga mutane miliyan 115 da aka tabbatar da cutar tun barkewarta a Wuhan ta kasar China a shekarar 2019.
Wasu manyan kamfanonin harhada magunguna sun kera alluran rigakafi game da mummunar cutar, yayin da rarraba alluran ke gudana a duk fadin duniya.