Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar shirya aikin Hajji ta ƙasa ta fitar da sabon farashin kuɗin Hajjin Bana kamar haka:
Daga yau 24 ga watan Maris Maniyyata daga shiyyar Adamawa/Borno za su biya Naira milyan N8,225, 464.74
Maniyyata daga shiyyar Arewa za su biya Naira milyan N8, 254, 464.74
Sai maniyyata daga jihohin shiyyar Kudu za su biya Naira milyan N8, 454, 464.74.
Karamar kujera kuma ta tafi Naira miliyan 6.6.
Tuni dai majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta nuna damuwa gami da fargabar daƙile ‘yan Najeriya daga gudanar da aikin hajji a bana.