Yayin da ake shirye-shiryen soma aikin hajji gadan-gadan a ?asar Saudiyya, ana nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ?aruwa a birnin Makka da kewaye inda ake gudanar da ibadar ta hajji.
Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birnin mai tsarki gabanin somawar aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a.
Hukumomin ?asar kan yi tanadin na’urorin da za su taimaka wa maniyyata wajen rage zafin da suke fuskanta. Fiye da mutum miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajji a wannan shekara