Haƙurinmu Ya Ƙare Maza Muke Buƙata – Matan Gidan Yari

Matan dake a gidan gidajen yarin kasar Kenya sun roki gwamnatin kasar da ta bar samarinsu su dinga saduwa dasu in sun kawo musu ziyara.

Wasu daga cikin matan sun koka kan cewa an yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai ne kuma suna bukatar a riƙa biya musu bukata.

Mai magana da yawun ƴan Matan gidan yarin Sofia Sweleh wadda aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai ce ta shaida hakan a madadin sauran ƴan uwanta da suke tsare a tare.

Bincike ya nuna cewar ana samun irin wadannan matsaloli sosai a gidajen Yari sakamakon tsawon lokaci da fursunonin ke dauka suna tsare, lamarin da ya sanya ake samun faruwar luwadi da maɗigo a tsakaninsu.

A wani rahoto na baya bayanan da wata kungiyar dake rajin kare hakkin Dan Adam dake Amurka ta fitar, ta nuna cewar fursunoni da dama suka samu sauya yanayi da shiga wata sabuwar rayuwa dalilin cudanya da wasu baƙi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply