Gyaran Tsarin Mulki; Shirme Da Shiririta Ne – Dattawan Arewa

Kungiyar Dattawa Arewa (NEF), karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi, ta yi fatali da shirin Majalisar Tarayya na gyaran Kundin Tsarin Mulki a matsayin shiririta da bata lokaci.

Kungiyar ta bukaci Majalisar da ta bar batun domin tarin rahotanni da shawarwarin gyaran Kundin Tsarin Mulkin da aka yi a baya da ke gabanta da bangaren Zartarwa sun wadatar idan har da gaske suke so su magance matsalolin Najeriya.

“Mun yi amannar cewa yawan sake gyaran da Majalisar Dattawa ke yi ba shi da fa’ida, face barnar lokaci da dukiya, don haka kada ’yan Najeriya su yarda da shi a wannan mawuyacin halin tattalin arziki da kalubalen da ba a taba samun irinsa ba.

“Babu wani abun a zo a gani da aka taba samu daga shirye-shiryen da aka yi a baya na magance matsalolinna siyasa da tattalin arziki a kasar nan.

“Majalisar Tarayya na bin makadi da rawa ne saboda haka kar a ba ta goyon baya a kan haka”, inji kakakin NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed.

Ya shaida wa taron manema labaran cewa rayuwar Najeriya a nan gaban ta ta’allaka ne a kan yadda kasar ta shirya magance manyan matsalolin da ke hana samuwar adalci da kuma tsari da shugabanci nagari; Sannan tsaron lafiyar ’yan kasa da kuma tsarin zaben mai inganci da wanzuwar fahimtar juna a tsakanin dukkanin bangarorin kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply