Gyaran Tarbiyya Muke Yi Wa Matasa – Nomiis Gee

Shahararren mawaki Nomiis Gee wanda ke gabatar da shirye-shirye irinsu “Zafafa Goma” da shirin “Hip Hop” a tashar Arewa24 ya bayyana cewa babu abinda shirye shiryensa ke yi sai gyaran tarbiyya ga matasa.

Matashin mawakin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar Aminiya inda ya musa zargin cewa shirye-shiryensa na lalata tarbiya.

“Dumbin jama’a sun shiryu ta dalilin shirye-shiryen da mu ke watsawa”

“Mahassada da ‘yan bakin ciki ne kawai ke sukar shirye-shiryenmu. Kun taba ganin wurin da aka hana nishadantarwa a duniya?

Ni kullum ina kalubalantar al’umma cewa su fito su bayyana wurin da yake bata tarbiyyar guda daya.

Abinda zan fada kawai shi ne bakin ciki da wadansu ke yi, na je wani wuri da ba su je ba ko an san ni su ba a san su ba.

Wadannan mutane suna kallon DSTV a gidajensu ba tare da tacewa ba.

Haka kuma wayoyi ne a hannun ’ya’yansu wadanda suke shiga intanet su kalli abin da suke so.

Duk ba su tsaya sun duba wannan ba sai abin da muke nunawa wanda ke wa’azantarwa tare da amfanar da jama’a ta fuskoki da dama.

Ya kuma yi kira ga matasan da ke da fasahar waka da su kokarta wajen baiwa al’umma gudummawa daga baiwar da su ke da ita.

Ko mene ra’ayinku game da wannan magana da Nomiis Gee ya fada?

Labarai Makamanta

Leave a Reply