Kungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai rika tuntubar juna da aiwatar da abubuwan da aka cimma bayan, kammala taron inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da aka gudanar a Katsina.
An gudanar da taron ne da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya inda ?wararru da sauran masu ruwa da tsaki a shaanin tsaro suka yi gagarumar tattaunawa ta kwana biyu tare da cimma matsaya kan abubuwa da dama wadanda za su taimaka wajen magance matsalar tsaron da ke addabar yankin.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso yamman, kuma ya shaida wa BBC cewa taron ya sha banban da wadanda aka sha gudanarwa a baya.
Ya ce ganin irin fuskokin da suka halarci taron, hakan ya nuna musu cewar matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin ta dami kowa, wanda yasa mutanen da a baya suke yi wa lamarin ru?on sakainar kashi, yanzu kowa ya fahimci cewar dole ne a ha?a hannu wajen ganin an ?auki matakai da za su kawo ?arshen matsalar.
Gwamna Dikko Ra??a ya ce ‘Mun kafa sakatariya da ta ?unshi wakilcin mutum ?aya daga kowacce jiha da wakilan Majalisar Dinkun Duniya su biyar, inda za a fito da jadawalin yadda za a yi aikin da wadan za su yi, kuma ana sa ran gabatar da rahoton cikin mako uku, wanda bayan an samar za su zauna da Majalisar Dinkin Duniya daga nan gwamnomin jihohn kowa ya ?auki banagren da zai je ya mayar da hanakali wajen aiwatar da shi”
Sannan Dikko Ra??an ya ce sun fahimci cewar matsalar tasaron ba wai ta bindiga ce ko kwari da baka ba ne kadai, dole ne sai an samar da aikin yi da bun?asa tattalin arzikin al’umma. ta yadda za a bunkasa harkokin noma, wanda ko su masu garkuwa da mutanen idan aka samar da wa?annan abubuwan zasu futo su zo su kashe ku?a?en da suka sata, amma yanzu saboda gazawar hakan basa iya futowa su kashe su.
“Mun fa?a wa juna gaskiya mu gwamnoni ga kurakuren mu, kowa ga nasa, sannan ga yadda muke ganin ya kamata a magance wannan matsala, haka su ma Majalisar Dinkin Duniya sun gaya mana ga yadda suke ganin za a shawo kan matsalar, mun kalli mastalolin a bayyane” inji shi.
Kungiyar gwamnonin Arewa maso yammacin Najeriya da hadin guiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya suka shirya taron wanda aka kammala a ranar Talatar da ta gabata, wanda aka gudanar a jihar Katsina.
Cikin masu halartar taron har da mataimakin shugaban kasa Khashim Shatima da manyan jami’an tsaro da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.