Gwamnonin Arewa Sun Bar Jaki Sun Koma Dukan Taiki – Matasan Arewa

Gamayyar ?ungiyoyin Matasan Arewa 19, ?ar?ashin jagorancin Alhaji Nastura Ashir Shereef, sun bayyana taron da kungiyar gwamnonin Arewa suka gudanar tare da Sarakunan Arewa kwanan nan a Kaduna, a matsayin wani zama da ya yi hannun riga da muradun jama’ar Arewa.

Matasan sun bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da suka kira wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake garin Kaduna.

Matasan sun bayyana cewar babban abin mamaki ne da takaici a taron gwamnonin Arewa, inda gaba ?aya basu yi magana akan matsalar da ke addabar yankin ba na ta?ar?arewar tsaro da garkuwa da mutane, sai kawai suka ?ige da surutu akan maganar Zanga-Zangar Endsars da batun Soshiyal Midiya.

“Irin wa?annan halaye da gwamnonin Arewa suke nunawa shine ya ke sanyawa ake wulakanta ‘yan Arewa musanman a kudancin ?asar, ake ?aukar ‘yan arewa a matsayin wawaye marasa alkibla”.

Matasan na Arewa sun ?alubalanci gwamnonin na Arewa da yin koyi da gwamnan jihar Ribas Wike wanda ya fito fili ya la’anci ?ungiyar Tsagerun Inyamurai IPOP, ya shelanta haramta ayyukan su a Jihar.

Daga ?arshe matasan na Arewa sun shawarci gwamnonin Arewa su mayar da hankula wajen gyaran matsalolin da ke addabar yankin, su ha?a kawunan su wuri guda domin kai wa ga nasarar da ake nema.

Related posts

Leave a Comment