Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Gwamnonin APC Na Ƙoƙarin Ganin Bayana – Oshiomole

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, a ranar Litinin a Abuja.

Ya zargi gwamnonin APC da amfani da darakta janar na kungiyar, Salihu Lukman, don kai shi kasa.

A yayin martani ga wani hasashe da kungiyar ta yi na cewa zai koma shugabancin jam’iyyar, Oshiomhole ya zargi gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi, da nada Lukman a matsayin shugaban kungiyar shi kadai.

Ya sanar da manema labarai cewa ba zai shiga kazamin fadan da Lukman ke nemansa da shi ba.

“Abinda basu gane ba shine ba kujerar shugaban jam’iyyar bace ta sa na zama abinda na zama. Na yi aiki a masana’antar masaka inda na zama babban sakataren masana’antu na dukkan Najeriya kuma na zama shugaban kungiyar kwadago.

“Babu wani kauye da zan shiga jama’a basu sanni ba kuma hakan nayi amfani da ita wurin wuce iyayen gidansa a Edo.

“A don haka ni bana iya mayar da martani ga masu surutu kuma wadanda kungiyar gwamnonin ce ta daukesu aiki.

“Ya yi takarar majalisar wakilai a Makarfi ya fadi. Ya yi takara da gwamna El-Rufai kuma ya fadi yayin zaben fidda gwani kuma ya sha kaye kafin Fayemi ya zabesa.”

A baya mun ji cewa darakta janar na kungiyar gwamnonin APC, Dr Salihu Lukman, ya zargi cewa akwai shirin mayar da Adams Oshiomhole tsohuwar kujerarsa ta shugabancin jam’iyyar APC.

Ya yi ikirarin cewa akwai kokarin da ake yi don zagon kasa ga kwamitin rikon kwarya na Mai Mala Buni.

DG Lukman a wani bayani da yayi a kan kwamitin rikon kwaryan, ya ce: “komai ana yin shi ne don ganin an juya siyasar cikin gida don samun yadda Oshiomhole zai haye kujerar shugabancin jam’iyyar.”

Lukman, wanda babban mai adawa ne da salon Oshiomhole, ya ce daga cikin wani bangare na kokarin shine amfani da zaben Edo wajen cin zarafin shugabannin APC

Exit mobile version