Gwamnoni Za Su Yi Taron Dangi Wajen Yakar Yunwa A Najeriya

IMG 20240310 WA0422

Gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Najeriya sun ce sun bullo da dabaru da daukar matakai daban-daban domin kawo karshen matsalolin tattalin arziki da karancin abinci a jihohinsu.

A cikin wani rahoto mai dauke da sa hannun mukaddashin shugabar sashen yada labarai na kungiyar gwamnoni (NGF), Halimah Salihu Ahmed, ta ce gwamnonin sun dukufa wajen kawo karshen radadin da ‘yan kasa ke ciki.

Idan baku manta ba, a watan Fabrairu ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin a Abuja, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi tashin farashin kayan masarufi, tabarbarewar tattalin arziki.

Rahoton na NGF ya bayyana cewa gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar, Abdulrahman Abdulrazaq tare da hadin gwiwar gwamnoni irinsu Agbu Kefas na jihar Taraba; Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo; da kuma Ahmed Ododo na jihar Kogi sun yi ta kokarin ganin an kara habaka fannin noma.

A cewarsu, hakan zai yiwu ne ta hanyar yin amfani da ma’aikatar noma ta kasar, inda za asamar da hanyoyin da za a samu wadataccen abinci.

Najeriya dai kasa ce mai yawan girman kasa da jama’a, amma noma ya zama abu mai wahala ga da yawan ‘yan kasar saboda wasu dalilai.

Hakazalika, rahoton ya bayyana yadda gwamnatoci a jihohin kasar nan suka fara aikin tabbatar da kayan abinci ya sauka don amfanin talakawa. An buga misali da yadda a baya gwamnatin Kano ta garkame dakunan ajiyar ‘yan kasuwan da ake zargi da Karin farashi ba gaira babu dalili. Ba Kano ba, jihohi irinsu Yobe, Zamfara, Niger, Ekiti da Legas duk sun dauki matakai don ganin an shawo matsalar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply