Gwamnatinmu Ta Yi Rawar Gani Wajen Ceto Jama’a Daga Talauci – Buhari

Shugaban ?asa Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa tayi namijin kokari wajen ya?ar talauci zahiri da badini a Najeriya, wanda jama’a kowa ya shaida hakan a kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin kai tsaye da ya yi wa ‘yan kasa a daren ranar Alhamis. Acewarsa gwamnatinsa ta dauki matakai da ?ir?irar tsare-tsare wanda akayi musamman don cigaban matasa, mata da wanda abin ya shafa a cikin al’umma.

“Wannan na daga cikin babban tsarin mu na ceto y’an Najeriya miliyan 100 daga k’angin talauci nan shekaru 10 masu zuwa.
“Mun ?ir?iri hannun jari na naira biliyan 75 don samar da damammaki ga matasa da masu k’ananan da matsaikaita masana’antu (MSME) wanda aka fi sani da survival fund.

“Biyan ku?in albashin wata uku na ma’aikata dubu 100, na ?anana da matsakaitan masana’antu, biyan kudin rijistar CAC ga mutane dubu 250 da makamantansu.
“Wannan ?ari ne akan tsaruka irinsu; Farmer moni, Tradermoni, Marketmoni, N-power, N-Tech da N-Agro.”

Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga masu zanga zangar da suyi tunani akan irin kokarin da yake na inganta rayuwar matasa irinsu. “A wannan yanayin nake kira ga masu zanga zanga da suyi amfani da irin tunanin da muke na inganta rayuwarsu, su kuma sauke fushi tare da kaucewa bata gari wajen yin amfani dasu don kawo hayaniya da haddasa fitina da nufin lalata tsarin damokradiyya,” a kasar nan.

Related posts

Leave a Comment