Gwamnatina Ta Kawo Cigaban Da Gwamnatocin Baya Ba Su Kawo Ba – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bawa aiyukan raya kasa muhimmanci, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da ba kamfanonin cikin gida kwagilolin gudanar da ayyuka, sakamakon yin hakan zai samar da aiyuka ga dubban ‘yan Najeriya.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin bude katafaren ginin cibiyar sabuwar hukumar gwamnati; NCDMB (Nigerian Content Development and Monitoring Board), a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

“Wannan ginin bene mai tarihi, mai hawa 17, ya kasance daya daga cikin manyan aiyuka da wannan gwamnati ta yi domin kirkirar aiyuka da ma su saka hannun jari. “Akwai cibiyar samar da wuta mai karfin 1megawatts da Kuma dakin taro na zamani mai cin mutane 1000.

“Kaddamar da wannan katafaren aiki ya nuna cewa gwamnatinmu ta kafa tarihi a yankin kudu ma so kudu mai arzikin man fetur dama ƙasa baki daya.
“Haƙiƙa gwamnatin mu ta yi abubuwan da gwamnatocin baya ba su yi ba a kasar nan”.

“An yi facaka da kudadenku a baya ba tare da yi mu ku wasu aiyuka ba. Ina tabbatar mu ku cewa wasu manyan aiyukan na nan tafe,”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply