Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Tsarin Magance Zaman Banza Ga Matasa

Minista a Ma’aikatar kimiyya da fasaha Dr. Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin tarayya za ta inganta rayuwar matasa 13, 000 a Najeriya domin kawo karshen rashin aikin yi da zaman banza a tsakanin su.

Ministan Onu ya ƙara da cewa za a dauki wadannan matasa aiki a bangarori uku na gwamnati da ake da su.
Ministan ya bayyana haka ne a garin Abakaliki, jihar Ebonyi, wajen kaddamar da shirin daukar aikin ESPWP da gwamnati za ta yi.

Ogbonnaya Onu ya ce an kawo wannan shiri ne domin inganta ayyukan kananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya a kasar.

Dr. Onu ya cigaba da cewa amfanin wannan shiri da gwamnatin APC ta dauko shi ne a tabbatar da dorewar ayyukan da gwamnatin ta ke yi. “A kowace karamar hukuma aikin da za ayi ya sha ban-bam, amma makusudin shi ne tabbatar ana yin ayyukan gwamnati da kyau, kuma suna dorewa.” Inji Onu.

Ya yi kira ga wadanda za su amfana da wannan shiri su nuna jajircewarsu da nufin su samu abin dogaro. Bayan haka, Onu ya roki ‘yan kasuwa masu zaman kansu, su dauki matasan da za an horas dasu aiki bayan sun samu kwarewa da sanin makaman aiki.

Labarai Makamanta