Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Gandun Kiwon Jakuna

Cibiyar bincike don bunkasa kiwon dabbobi a Najeriya NAPRI da hadin gwiwar wasu abokan hulda za su yi aiki tare domin samar da gandun kiwon jakuna a jihohin Bauchi da Ebonyi.

Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya ruwaito shugaban cibiyar Farfesa Abdullahi Mohammed na cewa sun kulla wata yarjejeniya da abokan huldarsu a watan Fabrairu domin samar da jakai miliyan biyu a Najeriya nan da shekara biyar zuwa 10.

Farfesan ya ce shirin zai iya samarwa da kasar kudin shiga da suka kai dala biliyan biyu a ko wacce shekara.

Bayan bunkasa kiwon jakai da shirin zai yi, zai kuma taimaka wajen fadada komar tattalin arzikin kasar a bangaren kiwo da harkar noma.

Labarai Makamanta

Leave a Reply