Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rage farashin mai zuwa N100 kan kowace lita, kamar yadda Jaridar Vanguard News ta ruwaito.
A cewar Enang, gwamnatin tarayya ta kuma kammala shirye-shiryenta na gudanar da taron kasa kan hada aikin matatar mai ta zamani domin inganta karfin aikin da kuma rage farashin albarkatun mai.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata a Abuja.
Tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa, Fadar Shugaban Kasa za ta gudanar da taron a ranakun 16 da 17 ga Maris.
Mista Enang ya lura cewa sakamakon taron zai taimaka wajen karya farashin kasar na albarkatun mai.