Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Titin Dogo Daga Kano Zuwa Nijar

Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi fashin baki kan kwangilar ginin layin dogo daga Najeriya zuwa jamhurriyar Nijar da gwamnatinsu ta bada.

Mun kawo muku rahoton cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da fitar da Dallar Amurka biliyan 1.95 domin ginin layin dogo da zai tashi daga Kano-Dutse (Jigawa)-Katsina-Jibia zuwa Maradi (Jamhuriyar Nijar).

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a gidan gwamnati bayan taron Majalisar da Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ya kuma ce Majalisar ta amince da fitar da Naira biliyan 3 don tsarawa, gini, samarwar da gwajin babban na’urar gyara da daukan kaya mai nauyin ton 150 domin ayyukan gaggawa yayin aikin layin dogon.

Hakan ya janyo cece-kuce cikin ‘yan Najeriya musamman ‘yan bangaren kudancin kasar inda suke zargin shugaba Buhari da bannatar da makudan kudade wajen ginawa jamhurriyar Nija layin dogo amma babu ko daya a kudu.

Amma Garba Shehu ya yi fashin bakin kan lamarin inda yace yarjejeniya akayi tsakanin Najeriya da Nijar domin gina layin dogon.
“A shekarar 2015, an yi yarjejeniya tsakanin Najeriya da Nijar karkashin jagorancin hukumar hadin kai tsakanin Najeriya-Nijar domin ginin layin dogo “Kano-Katsina-Maradi,
“Bisa ga yarjejeniya, kasashen biyu zasu gina nasu layin dogo daga cikin kasashensu a hadu a iyaka Maradi.” “Manufar layin dogon shine cin gajiyar ma’adinai, da amfanin gona.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply