Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rancen Kuɗaɗen Ajiyar ‘Yan Najeriya Dake Banki

Duk da rashin amincewar masu hannun jari, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kudade, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden ‘yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba’a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba’a bibiya ba.

Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin Shekarar 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.

Ƙarkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za’a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan da mutane wanda suka kai shekaru shidda ba’a waiwaya ba.

Gwamnati tace duk kudaden da ba’a bibiya ba za’a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna ‘Unclaimed Funds Trust Fund’.

Yanzu gwamnatin na shirin aron wadannan kudaden dake cikin asusun.
“Za’a tura wadannan kudade asusun lamunin kudaden da ba’a bibiya ba kuma gwamnati zata iya karba bashi daga ciki amma zata biya a duk lokacin da mai hannun jarin ya bukata,” dokar ta tanada.

Labarai Makamanta