Gwamnatin Tarayya Za Ta Bullo Da Sabbin Matakai Domin Saukaka Wa ‘Yan Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa majalisar kula da Tattalin Arzi?i a Najeriya ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta ?auka don samar wa ‘yan ?asar sau?in rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.

Majalisar ta sanar da matakan ne a ?arshen taron wata-wata da ta yi a ?ar?ashin jagorancin mataimakin shugaban ?asar Kashim Shettima.Taron na tsawon kimanin sa’a shida ya fi mayar da hankali a kan batutuwa guda biyu da suka fi tasiri wajen jefa ‘yan ?asar cikin mawuyacin hali. Wato janye tallafin mai da kuma karyewar darajar naira.

Bayan tafka muhawara da musayar yawu, taron ya amince da ?aukar wasu matakai na gaggawa domin tsamo ‘yan Najeriya musamman mafi ya rauni daga cikin halin da suka shiga. Daga ciki akwai bu?atar kowacce jihar ta tsara yadda za ta samar wa jama’arta sau?i ko dai ta hanyar raba tallafin ku?i ko kuma ta hanyar da ta fi dacewa.

Haka ma an amince da bai wa ma’aikatan gwamnati tallafin ku?i a kan albashinsu, tsawo wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma’aikata da ‘yan fansho dukkan basukan da suke bi.Wa?annan in ji majalisar za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da rarar ku?in da gwamnati za ta samu saboda janye tallafin man fetur da kuma daidaita harkar canjin ku?i.

Bugu da ?ari, taron ya amince da aiwatar da wani tsari na sauya makamashin da ababen hawa suka fi amfani da su daga man fetur wanda ya yi tsada yanzu zuwa wani nau’in iskar gas da ake kira CNG a ta?aice wanda Najeriya ke da shi mai tarin yawa kuma ga arha.Jihohin ?asar sun amince za su fara juya motocin jigilar ma’aikata zuwa masu amfani da iskar gas.Amma duk wa?annan matakai, sai bayan an aiwatar da shirin raba kayan abinci ga ?aukacin jihohin ?asar domin sauko da farashinsa.

Related posts

Leave a Comment