Gwamnatin Tarayya Za Ta ?auki Nauyin Karatun Tsoffin Boko Haram A Waje

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun bayyana tattaunawa da ake yi game da sabon kudirin da aka kawo a majalisa domin ilmantar da tsofaffin ‘yan ta’addan Boko Haram a Najeriya a Waje.

Wannan kudiri zai yi kokarin sauya tunanin tubabbun ‘Yan Boko Haram, sannan a ba su matsuguni.

Hukumomi irinsu UBEC da TETFund da gwamnatocin jihohin Arewa maso gabas ne za su kawo kudin da za ayi wa tubabbun ‘yan ta’addan hidima.

‘Yan majalisa sun kira wannan kudiri da: A Bill for the Establishment of the National Agency for the Education, Rehabilitation, De-radicalisation and Integration of Repentant Insurgents in Nigeria and for Other Connected Purposes’ A ranar Alhamis da ta gabata, aka saurari wannan kudiri a karon farko, har ya samu karbuwa.

Shugaban kasa ne zai nada shugaba da zai kula da wannan ma’aikata, wanda daga cikin aikinsa har da tura tsofaffin ‘yan ta’adda karatu a kasashen ketare.

Kudirin ya ce za a cire 0.5% daga cikin kason jihohin Arewa maso gabas, sannan hukumomin TETFund da UBEC za su ba hukumar 1% daga kasonsu.

Related posts

Leave a Comment